Dakataccen gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ne ya yaba da ƙoƙarin Shugaba Bola Tinubu na samar da maslaha a jiharsa.
Fubara ya bayyana haka ne a wani taro da magoya bayansa suka shirya a Fatakwal, inda ya ce matakin na Tinubu ya taimaka sosai, wanda a cewarsa hakan ne zai sa cigaba da kasancewa a matsayin gwamna.
Tashar Channels ta ruwaito shi yana kira ga magoya bayansa da su yi godiya ga shugaban, inda ya ƙara da cewa ba don Tinubu ya shiga tsakani ba, da rikicin ya wuce abin da ake tunani.
Fubara ya kuma yi godiya ga magoya bayansa da sauran ƴan Najeriya bisa nuna masa ƙauna.