Rundunar ‘Yan Sanda ta bayyana kashe wani Shugaban manyan barayi a jihar Rivers

0 173

A Jihar Rivers kuma, rundunar ‘yan sanda ta bayyana kashe wani da ake zargi da zama shugaba kuma manyan barayin mutane da ke addabar yankin, David Kamalu, wanda aka fi sani da “M-Kaze”, a wani samame da aka kai Rumuodogo One, karamar hukumar Emohua.

Kakakin ‘yan sanda na jihar, Grace Iringe-Koko, ta ce Kamalu ya mutu a musayar wuta da jami’an tsaro da safiyar jiya Juma’a, bayan kwashe kwanaki ana tattara bayanan sirri game da shi.

Ta bayyana cewa Kamalu ya dade yana jagorantar gungun masu garkuwa da mutane, har ma da kashe wani jami’in tsaro na yankin da aka fi sani da “Hunter Commander” a watan Janairu. Rundunar ‘yan sanda ta bukaci al’umma da su kai rahoton duk wanda aka gani da raunukan harbin bindiga, yayin da ake ci gaba da farautar sauran ‘yan gungun da suka tsere da raunuka.

Leave a Reply