Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta sanar da mutuwar mutane 366 daga cututtukan zazzabin Lassa da sankarau a jihohi 24 na ƙasarnan daga watan Janairu zuwa 18 ga watan Mayu.
A cewar rahoton hukumar, an tabbatar da mutum 733 da suka kamu da zazzabin Lassa daga cikin mutane 5,118 da ake zargi da kamuwa a ƙananan hukumomi 95 a jihohi 18, inda cutar ta fi shafar matasa ‘yan shekara 21 zuwa 30.
Cutar ta fi kamari a jihohin Ondo, Bauchi da Edo, wadanda suka haɗa kaso 72 cikin ɗari na duka masu cutar, yayin da cutar sankarau ta fi shafar yara ‘yan shekaru 5 zuwa 14, musamman a arewacin kasa. Hukumar ta ce an kafa Cibiyar Aikin Gaggawa tare da haɗin gwiwar ma’aikatar lafiya, hukumar rigakafi ta kasa da sauran abokan haɗin gwiwa don daƙile yaduwar cututtukan.