A cewar wata sanarwa da fadar shugaban kasa ta fitar da daddare, matakin ya biyo bayan rahoton da hukumar NEMA ta gabatar kan bukatar daukar matakan gaggawa domin taimakawa wadanda abin ya shafa.
Rahoton ya ce ruwan sama mai karfi da aka yi tun daga ranar Laraba har zuwa Alhamis ya lalata gidaje tare da sanadiyyar mutuwar muatne da dama, lamarin da ke kawo cikas ga kokarin tantance adadin mamatan. Shugaba Tinubu ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan da suka rasa ‘yan uwa, yana mai tabbatar da cewa kayan agaji da mafaka na wucin gadi na ci gaba da isowa domin tallafawa wadanda suka rasa matsugunnai.
Shugaba Bola Tinubu ya umarci bude cibiyar bayar da agajin gaggawa a jihar Neja bayan iftila’in ambaliya da ya hallaka akalla mutum 115 a yankin Mokwa.