Kwamitin majalisar Wakilai ya gayyaci shugaban Jami’ar Tarayya ta Dutsin-Ma

0 101

Kwamitin majalisar wakilai da ke kula da korafe-korafen jama’a ta gayyaci shugaban Jami’ar Tarayya ta Dutsin-Ma da ke jihar Katsina, Farfesa Armayau Hamisu Bichi da ya bayyana a gabanta domin amsa tambayoyi kan zargin ‘rashin iya jagoranci’ da ake yi masa.

Gayyatar tasa ta zo ne bayan wani mai suna Shehu Abubakar Tadda ya shigar da korafi kan yadda Farfesa Bichi yake tafiyar da salon shugabancinsa wanda a cewarsa bai dace ba.

Kwamitin ya buƙaci shugaban jami’ar da ya bayyana a gabansa a ranar Laraba 18 ga watan Satumban.

Majalisar wakilan ta ce gayyatar tana  sashe na 88 da kuma 89 na kundin mulkin kasar, wanda ya ba ta damar bincike kan batutuwa da suka shafi al’umma.

Haka kuma, majalisar ta buƙaci wanda ya shigar da korafin da shi ma ya bayyana a gabanta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: