Kwamittin ‘yan sanda na kasa ya bayyana Dutse a matsayin hedikwatar jiha mafi zaman lafiya a Najeriya

0 324

Gwamna Mallam Umar Namadi ya karbi bakuncin shugabannin kwamitin ‘yan sanda na kasa, wadanda suka kai masa ziyarar ban girma a ofishin sa dake Dutse fadar gwamantin jihar Jigawa.

Shugaban kwamittin na kasa, Alhaji Ibrahim Olaniyi, ya ce sun je Dutse ne domin taya gwamnan murnar nasarar zaben da ya samu a matsayin gwamnan jihar.

Kwamittin ya bayyana Dutse a matsayin hedikwatar jiha mafi zaman lafiya a Najeriya, inda suka ce tabbas hakan ya tabbata kuma ya dore saboda kyakkyawan shugabanci na yanzu a jihar.

Da yake mayar da jawabi, Gwamna Umar Namadi ya bayyana matukar jin dadinsa da ziyarar da kwamittin hukumar na kasa ya kai masa, inda ya bayyana kwamitin a matsayin mai matukar muhimmanci wajen taimakawa da kulla alaka mai kyau tsakanin al’umma da ‘yan sanda. Ya kuma yi alkawarin cewa gwamnati za ta ci gaba da baiwa kwamitin goyon baya domin cimma manufofinsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: