Labari Mai Daɗi: Nan Da Lokaci Kaɗan Matatun Fetir Ɗin Najeriya Zasu Dawo Aiki Baki Ɗaya

0 451

Gwamnatin Tarayya tace ta fara aikin gyaran matatun man fetur, farawa da matatar man fetur ta Fatakwal domin cimma burin shekarar 2023 na ganin cewa dukkan matatun na aiki yadda ya kamata.

Shugaban kamfanin man fetur na kasa NNPC, Mele Kyari, shi ne ya bayyana haka yayin da yake magana akan cin gajiyar arzikin mai da iskar gas domin cigaban kasa.

Yayi magana ne yayin taron shekara-shekara na kungiyar ‘yan jaridu dake dauko rahoto daga masana’antun man fetur.

Mele Kyari yace hukumar ta NNPC ta bawa kanta wa’adin shekaru 3 domin bibiyar ayyukan matatunta, tare da tallafa musu.

Yace Najeriya tana nan a matsayin kasa mai shigo da dukkan albarkatun man fetur. Yace hakan ya kasance ne saboda halin da matatun suke ciki, tare da rashin masu zuba jari a bangaren tace mai.

Mele Kyari daga nan sai ya jinjina bukatar samar da yanayi mai kyau domin jawo hankalin masu zuba jari. A nasa jawabin, shugaban kungiyar masu kasuwancin sarrafa man fetur, kuma daraktan kamfanin ExxonMobil a Najeriya, Mista Paul McGrath, ya nuna damuwa akan kudaden da ake kashewa wajen gudanar da kasuwanci a kasar.

Paul McGrath sai ya bukaci gwamnati da masu hannu a harkar, da su lalubo hanyoyin da za abi wajen rage yawan kudaden da ake kashewa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: