Lallai Ya Kamata A Yiwa Dokar Fyaɗe Garambawul – Kungiyoyin Kare Haƙƙin Mata

0 254

Kungiyoyi masu fafutukar kare hakkin yara da mata a ƙasar nan sun bukaci a yi wa dokar hukunta masu fyade garambawul tare da yi musu hukunci mai tsanani.

Hakan na zuwa ne a lokacin da ake ci gaba da alhinin mutuwar wata matashiya mai suna Uwaila Omozuwa wacce ta mutu bayan da aka yi mata fyade a cikin wani coci a birnin Benin da ke jihar Edo.

A wani al’amari mai kama da na matashiyar, a jihar Jigawa ma an kama wasu maza su 11 da aka gano cewa suna yin lalata da wata karamar yarinya ‘yar shekara 12, da na 12 da yake shirin yi mata fyaden.

Tuni dai Gwamnatin Tarayya ta umarci ‘yan sanda da su gudanar da bincike kan al’amuran biyu.

A shafukan sada zumunta ma, mutane da dama na ta nuna bacin ransu da kuma kokarin kwato wa matashiyar da kuma yarinyar ‘yancinsu, tare da kawo karshen matsalar fyade a ƙasar nan.

Batun aikata fyade ga kananan yara na ci gaba da addabar al’umma musamman a arewacin ƙasar nan inda a lokuta da dama a ke zargin hukumomi da gazawa wurin hukunta wadanda a ke zargi.

Majalisar dattawar kasar nan ta bayyana cewa nan ba da jimawa ba za ta samar da kotuna na musamman domin hukunta masu aikata irin wannan muggan laifukka.

Masu fafutuka da dama sun yi ta koke-koke a kan irin yanayin da yara mata har ma da maza ke shiga.

Shugabar gidauniyar Arrida da ke fafutukar kare yara da mata da aka ci zarrafinsu, Rabi Salisu Ibrahim, ta ce kullum sai an kira su a kan ta’asar yi wa yara lalata.

“Ko yau da safe sai da aka kirani kan wani yaro dan shekara 4 da aka yi wa fyade.”

Ƙasar nan dai na cikin jerin kasashe goma da mata ke rayuwa cikin matsanancin hali na yawaita barazanan cin zarrafi da suka hada da yi musu fyade da dai sauransu.

A nata bangare, shugabar gudanarwa ta kungiyar WRAPA mai fafutukar neman ci gaba da kare hakkin mata, Saudatu Mahdi ta ce akwai dokokin hukunta masu aikata irin wannan laifi amma ana samun matsaloli wajen aiwatar da su inda ta bukaci hukumomin kasar su ba da gudunmuwa wajen karfafa ma’aikatun kiwon lafiya da sauran hukumomi daga matakin farko zuwa ga tarayya.

Da muka tuntubi dan majalisar wakilai Yunusa Abubakar mai wakiltar mazabar Yamaltu Deba na jihar Gombe, kan matakin da ake shirin dauka kan aika-aika na fyade, ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba majalisar dattawa za ta samar da dokar kafa kotuna na muamman domin hukunta masu laifi.

Ita ma jarumar fina-finan Hausa kuma mai fafutukar kare ‘yancin yara da mata Mansurah Isah, ta bayyana cewa a ganinta “lokaci ne yanzu da ya kamata iyaye mata a Arewacin ƙasar nan su koya wa mata da maza me ake nufi da fyade”.

Dokar manyan laifuffuka a ƙasar nan ta bukaci a yankewa duk wanda ya aikata laifin fyade hukuncin rdaurin ai-da-rai kuma duk wanda ya yi yunkurin yin fyade hukunci zaman gidan kaso na shekara 14.

Leave a Reply

%d bloggers like this: