Ma’aikatar Harkokin Al’adu da Yawon Shakatawa ta ƙaddamar da sabon shiri don bunkasa masana’antu

0 502

Ma’aikatar Harkokin Al’adu, Yawon Shakatawa da Tattalin Arzikin Kirkira ta ƙaddamar da wani sabon shiri na tallafin da za a raba ta hanyar asusun Creative Economy Development Fund.

Minista Hannatu Musawa ta ce wannan shiri wani ɓangare ne na cika manufar Sabunta Fata ta Shugaba Tinubu, domin bunƙasa ayyukan yi da fitar da al’adun Najeriya zuwa duniya.

Za a ba da lamuni, da jari da tallafi ga masu sana’o’in kirkira irin su fina-finai, da kaɗe-kade, da tufafi, da fasaha, da bugun littattafai da yawon buɗe ido.

Ana sa ran rabon kuɗin zai fara ne daga watan Janairu 2026, bayan kammala matakin tantancewa da shigar da ayyuka daga watan Yuni zuwa Disamba 2025.

Leave a Reply