JAMB ta bayyana cewa daga cikin ɗalibai 40,247 da suka rubuta jarabawar UTME ta 2025, mutum 467 ne kawai suka nuna bajinta

0 779

Hukumar JAMB ta bayyana cewa daga cikin ɗalibai masu ƙananan shekaru 40,247 da suka rubuta jarabawar UTME ta 2025, mutum 467 ne kawai – kimanin kaso 1.16 cikin ɗari – suka nuna bajinta da za a iya lissafta su a matsayin masu basira ta musamman.

Wannan na cikin sakamakon ɗalibai sama da miliyan daya da dubu dari tara da hamsin da biyar da aka fitar a bana.

Hukumar ta ce bincike na ci gaba kan wasu sassa na jarabawar da suka shafi ɗalibai makafi da waɗanda ke cikin ƙungiyar JEOG. Ta kuma bayyana cewa sama da ɗalibai 97 sun tafka laifukan jarrabawa, dalibai 2,157 suna fuskantar bincike, yayin da ɗalibai 71,701 ba su bayyana wajen jarrabawar ba

Leave a Reply