Babban Bankin Duniya ya shawarci gwamnatin tarayya da ta zage damtse wajen aiwatar da sauye-sauye da za su kare mafiya talaucin ‘yan Najeriya daga illar hauhawar farashi.
A cikin rahoton watan Afrilun bana, bankin ya bayyana cewa fiye da rabin al’ummar ƙasar – wato kashi 54 cikin 100 – na rayuwa cikin talauci, inda mutane miliyan 42 suka ƙara faɗawa ƙangin talauci tun daga shekarar 2018.
Duk da cewa sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta aiwatar sun fara kawo daidaito, hauhawar farashin kaya na cigaba da raunana ƙarfin sayen kayan masarufi da kuma rage samun kuɗin ma’aikata.
Bankin ya buƙaci a tabbatar da tsare-tsaren kariya ga talakawa da kuma bunƙasa sassan kiwon lafiya, da ilimi da ababen more rayuwa, musamman da kudaden da aka samu daga cire tallafin mai.