Shugaba Bola Tinubu na shirin ganawa da shugabannin kamfanonin samar da wutar lantarki domin magance bashin da ya kai Naira tiriliyan huɗu da suke bin gwamnatin tarayya.
Ministan Wuta, Adebayo Adelabu, ya bayyana cewa gwamnati za ta biya wani kaso mai tsoka daga cikin bashin cikin gaggawa, sannan ta biya sauran ta hanyar takardun lamuni.
Shugabanin kamfanonin wuta sun bayyana damuwarsu cewa rashin kuɗi yana hana su samun rance ko gyaran kayan aiki, wanda ke barazana ga rugujewar dukkan tsarin samar da lantarkin.
Gwamnatin na duba yiwuwar daina bayar da tallafi gaba ɗaya tare da neman jama’a su fahimci muhimmancin biyan kuɗin da ya dace da wutar da ake amfani da ita, musamman a wannan lokaci da farashin naira ke ta raguwa fiye da kima.