Magoya bayan jam’iyyar PDP kimanin 7,000 sun fice daga jam’iyyar zuwa ta APC bisa zargin cewa PDP ta gaza a duk sassan cigaba a Najeriya

0 98

A yayin da babban zaben shekarar 2023 ke kara gabatowa, lamarin sauyin sheka daga cikin manyan jam’iyyun siyasa biyu a jihar Sokoto na ci gaba da faruwa, yayinda magoya bayan jam’iyyar PDP kimanin 7,000 da suka fice daga jam’iyyar zuwa jam’iyyar APC, bisa zargin cewa PDP ta gaza a duk sassan ci gaba.

Hakan ya fito ne a wata sanarwa da mataimaki na musamman kan sabbin kafafen yada labarai, ga Sanata Aliyu Wamakko, Bashar Abubakar, ya fitar ya kuma bayyanawa manema labarai.

Sanarwar ta biyo bayan gagarumin sauya sheka da ke ci gaba da addabar jam’iyyar PDP mai mulki a jihar.

Wadanda suka sauya sheka, wadanda dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar, Ahmad Aliyu, ya tarbe su a karamar hukumar Wurno, sun hada da magoya bayan jam’iyyar PDP sama da 4,270 daga karamar hukumar.

Dan takarar gwamnan ya bayyana jin dadinsa kan dimbin magoya bayan da suka shiga jam’iyyar APC.

Aliyu, wanda ya wakilci shugaban jam’iyyar APC a jihar, Sanata Aliyu Wamakko, ya tabbatar wa ‘yan jam’iyyar da suka sauya sheka daidai wa daida.

Leave a Reply

%d bloggers like this: