Ambaliyar ruwa a kasar Sudan ta kashe akalla mutane 20 a cikin makon daya

0 97

Ambaliyar ruwa a kasar Sudan ta kashe akalla mutane 20 a cikin makon da ya gabata, kamar yadda hukumomin kasar suka sanar, lamarin da ya kara adadin wadanda suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa tun da aka fara damina a watan Mayu zuwa 134.

Ofishin Birgediya Janar Abdul-Jalil Abdul-Rahim, shugaban kwamitin tsaron fararen hula na kasar Sudan, ya ce karin mutane 120 sun jikkata sakamakon ambaliyar ruwa da ta afku a makon da ya gabata.

Ruwan sama kamar da bakin kwarya a cikin watan Agusta da farkon watan Satumba, ya shafe hanyoyi, gidaje, da muhimman ababen more rayuwa a fadin kasar, tare da katse hanyoyin samar da kayayyaki ga yankunan karkara dake bukatar agajin jin kai.

Bisa rahoton da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar na baya-bayan nan da aka yi, ambaliyar ruwan ta shafi kimanin mutane dubu 286,400, kana gidaje 16,900 suka lalace.

Hukumar ta ce a bana, mutane 74 ne suka nutse a ruwa, 32 kuma suka mutu a lokacin da gidajensu suka rufta, sai kuma wasu shida da suka mutu sakamakon wutar lantarki.

Kauyuka gabashi da yammacin kasar ne suka fi fama da mamakon ruwan sama a bana.

A shekarar 2020, ambaliyar ruwa da ruwan sama mai karfi ya kashe mutane kusan 100 tare da lalata gidaje sama da 100,000 a kasar ta Sudan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: