Mai martaba Sarkin Hadejia ya jaddada kudirin majalisarsa na tallafawa jami’an tsaro

0 252

Mai martaba Sarkin Hadejia shugaban majalisar sarakunan jihar Alhaji Dr Adamu Abubakar Maje ya jaddada kudirin majalisarsa na tallafawa jami’an tsaro domin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar da kasa baki daya.

Ya bayar da wannan tabbacin ne a lokacin da ya karbi bakoncin sabon kwamandan rundunar sojojin ta 26 ta armored Brigade a fadar sa.

Mai martaba Sarkin ya bayyana kyakkyawar alakar da ke tsakanin bangaren sarki da jami’an tsaro a jihar, inda ya kara da cewa za a ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa.

Sarkin ya bayyana jin dadinsa da fahimtar junan dake tsakanin jami’an tsaro da jama’ar jihar.

Tun da farko a nasa jawabin, sabon kwamandan Brigade, Birgediya Janar T.J Mackintosh ya ce ya je fadar ne domin gabatar da kansa da kuma neman albarkar sarki.

Ya kuma ba da tabbacin yin aiki kafada da kafada da Cibiyar Gargajiya domin cimma burin da aka sanya a gaba tare dayin alkawarin ba su goyon baya da hadin kai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: