Matatar mai ta Fatakwal za ta fara hako mai a cikin wata mai zuwa

0 194

Wani rahoto da kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) ya fitar ya nuna cewa matatar mai ta Fatakwal za ta fara hako mai a cikin wata mai zuwa, in ji karamin ministan albarkatun man fetur Heineken Lokpobiri.

Lokpobiri ya bayyana hakan ne a jiya laraba a gidan Talabijin na Channels a bikin cikar shugaba Bola Tinubu shekara guda.

Wannan dai ba shi ne karon farko da ministan zai gaya wa ‘yan Najeriya matatar Fatakwal za ta fara aiki ba. 

Duba da dimbin wa’adin da gwamnati mai ci ta yi a baya ba tare da an fara aiki da matatar mai na Fatakwal din ba, ministan ya ce bai kamata a dora masa alhakin gazawar wa’adin ba.

Bayan cire tallafin man fetur a jawabinsa na farko a ranar 29 ga watan Mayun 2023, farashin litar man fetur ya tashi daga N184 zuwa sama da Naira 600 a sassan kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: