Gwamnatin tarayya ta sake mika goron gayyata zuwa ga kungiyar kwadago domin ci gaba da tattaunawa kan mafi karancin albashi zuwa ranar Juma’a, kamar yadda manema suka bayyana jiyi labarai jiya a Abuja.
A watan Mayun da muke ciki Kungiyar Kwadago ta bai wa kwamitin har zuwa karshen wata da ya kammala tattaunawa kan sabon mafi karancin albashi.
A halin da ake ciki, Karamar Ministar Kwadago, Nkeiruka Onyejeocha, a jiya Larabar, ta yi kira ga kungiyoyin kwadago da su kasance masu la’akari da kishin kasa a kan bukatunsu a tattaunawar da ake yi kan sabon mafi karancin albashin ma’aikata.
Don haka ministar ta ce gwamnati ta fahimci cewa kalubalen tattalin arzikin da ‘yan Najeriya ke fuskanta a bangarori daban-daban don haka ta yi kira da a hada kai da masu ruwa da tsaki domin shawo kan lamarin.
Ta kara da cewa ganawar da kungiyoyin kwadago wani muhimmin mataki ne a yunkurin da ake yi na tabbatar da albashin ma’aikata na gaskiya da adalci.