Ana iya sayar da lita guda ta man fetur, wadda aka fi sani da Premium Motor Spirit (PMS) , a kan N234, in ji Manajan Darakta (GMD) na Kamfanin Mai na Kasa (NNPC), Malam Mele Kyari.

Kyari ya ce ana tunanin bullo da sabon farashin ne saboda kamfanin ba zai iya ci gaba da yin tallafi a duk wata na Naira biliyan 120 (Dala miliyan 263,248) ba, a lokacin rarraba kayan a farashin da ake amfani da shi a yanzu. PMS a yanzu ana sayar da shi tsakanin N163 da N165 kowace lita.

Kyari ya bayyana sabon farashin ne a wani taro karo na biyar na ankarar da Ministocin na musamman da Kungiyar Tattaunawar Shugaban Kasa ta shirya a Abuja, a jiya.

Ya ce NNPC na daukar bambancin kudin da ke rubuce a cikin litattafan kudi.

Kyari ya ce yayin da ainihin kudin shigowa ya kai lN234 kowace lita, gwamnatin tarayya na sayarwa ne kan N162 kowace lita.

Ya bayyana cewa NNPC ba za ta iya ci gaba da daukar nauyin wannan ba, ya kara da cewa ko ba dade ko ba jima ‘yan Nijeriya za su biya ainihin kudin man.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: