Majalisar Dattawa da ta Wakilai za su koma zaman majalisa a yau Talata bayan hutun kusan makonni shida da suka yi.

0 451

A Majalisar Tarayyar Najeriya kuwa, ‘yan majalisa daga Majalisar Dattawa da ta Wakilai za su koma zaman majalisa a yau Talata bayan hutun kusan makonni shida da suka yi

.

Shugaban masu rinjaye na Majalisar Dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele, ya bayyana cewa manyan abubuwan da za a mayar da hankali a kai sun hada da dokokin gyaran haraji, da matsalolin tsaro da rikicin siyasa a jihar Rivers, da kuma duba kundin tsarin mulki.

Dokokin harajin da za a duba sun hada da Nigeria Tax Bill 2024 da Tax Administration Bill da sauran su, inda wasu ‘yan majalisa daga Arewacin kasar ke nuna damuwa kan yadda sabon tsarin zai fi amfani ga wasu yankuna.

Sauran batutuwan da za a tattauna sun hada da kafa dokar ta baci a Rivers, wanda wasu gwamnoni da kungiyoyin lauyoyi suka soka, da kuma kokarin lalubo sabbin dabaru tare da hafsoshin tsaro domin dakile tashe-tashen hankula a Arewacin Najeriya.

Leave a Reply