Majalisar Dokokin Jigawa Ta Kai Rangadin Kananan Hukumomi 26 Don Tantance Harkokin Mulki da Kudi

0 369

Kwamatin kananan hukumomi na majalisar Dokokin jihar Jigawa ya Kai rangadi kananan hukumomi 26 kawo yanzu a kokarin da majalisa ke yi na tantance sha’anin mulki da harkokin Kudi a matakin kananan hukumomi.

Shugaban Kwamatin kuma wakilin mazabar Gwiwa Alhaji Aminu Zakari, ya bayyana haka a lokacin da Kwamatin ya ziyarci sakatariyar karamar hukumar Kiyawa.

Ya ce a lokacin irin wannan rangadi Kwamatin Yana la’akari da batun tattalin arziki da zamantakewar al’umma a matsayin alamomin cigaban rayuwa ko Kuma koma baya baya ga tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da kyakkyawar alakar aiki.

A nasa jawabin, shugaban karamar hukumar Kiyawa Malam Abdulhamid Ibrahim Balago ya lura cewa ziyarar Kwamatin za ta Kara musu azama wajen gudanar da ayyukan su kamar yadda yakamata.

Ya Kuma yabawa Gwamna Malam Umar Namadi bisa yadda ya ke baiwa kananan hukumomi damar su yayin da ya godewa shugaban majalisar Dokokin jihar Jigawa Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin bisa yadda majalisar ta ke gudanar da ayyukan da tsarin Mulki ya Bata dama.

Leave a Reply