NULGE Reshan Birniwa Ta Zaɓi Sabbin Shugabanni Don Jagorantar ƙungiya Na Shekaru Huɗu Masu Zuwa

0 850

Ƙungiyar ma’aikatan ƙananan hukumomi ta Najeriya (NULGE), reshen ƙaramar hukumar Birniwa, ta gudanar da zaɓen sabbin shugabanni da za su jagoranci ayyukan ƙungiyar na tsawon shekaru huɗu masu zuwa.

Comrade Ibrahim Musa – Shugaba

Musa Muhammad Kumsa – Mataimakin Shugaba

Sa’idu Abdullahi Birniwa – Sakatare

Garba Rabi’u – Ma’ajin Kuɗi

Hamza Muhammad – Mataimakin Sakatare

Ibrahim Muhammad – audito

Hadiza Musa Hassan – Shugabar mata

Da yake jawabi jim kaɗan bayan zaɓen, wakilin shugaban ƙungiyar na jihar Jigawa, Ibrahim Mu’azu Maigatari, ya shawarci sabbin shugabannin da su gudanar da aikinsu cikin gaskiya da rikon amana domin ci gaban ƙungiyar.

A nasa jawabin, shugaban ƙaramar hukumar Birniwa, Alhaji Shehu Baba Birniwa, ya bayyana jin daɗinsa kan yadda aka gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali da adalci.

A cikin jawabin godiya, sabon shugaban ƙungiyar, Comrade Ibrahim Musa, ya yi alƙawarin yin aiki tare da hukumomi da masu ruwa da tsaki domin cimma burin da aka sa gaba.

Leave a Reply