Majalisar Wakilai ta Dakatar da Shugaba Buhari Daga Ciwo Bashin Makudan Kudade

0 109

Majalisar wakilan kasarnan ta dakatar da  shirinnan na Gwamnatin tarayya na ciwo bashin kudade Dalar Amurka Biliyan 22.79, wanda aka sahale da fari.

Majalisar ta gabatar da jerin rahoton kwamatinta kan ciwo bashi na jadawalin karbar bashin Gwamnatin tarayya na shekarar 2016 zuwa 2018, a matsayin wanda zatayi la’akari dashi kawai a zamanta na Laraba.

Kakakin majalisar Femi Gbajabiamila shi ne ya bayyana janye sauraren shirin ciwo bashin, sai dai bai bayyana wani sabon lokaci da za’a saurara nan gaba ba.

Femi Gbajabiamila

Haka shi ma da aka tuntube shi kan dakatar da shirin ciwo bashin, mai baiwa ministar kudi shawara kan kafafen yada labarai, Mr. Yunusa Abdullahi, bai ce uffan ba.

Matakin dai na zuwa ne bayan da mambar majalisar Mr. Henry Nwawuba ya gabatar da takardar jin bahasi, dake adawa da shirin, wadda wata kungiyar masu ruwa da tsaki na yankin Kudu maso gabashi, suka aika masa.

A makon da ya gabata ne dai majalisar dokokin kasar nan ta amince da bukatar Gwamnatin tarayya, na ciwo bashin kudaden, duk da kalubalantar shirin da shugaban marasa rinjaye na majalisar Eyinnaya Abaribe ya yayi.

Haka kuma tuni shirin yasha suka daga miliyoyin yan Najeriya, sakamakon yadda masana tattalin arziki ke ganin hakan a matsayin abinda zai bautatar da yan kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: