Majalisar wakilai ta gayyaci ministocin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki da gwamnan CBN

0 57

Majalisar Wakilai ta Tarayya a ranar Alhamis ta gayyaci Ministan Kudi kuma Ministan na tarayya, Wale Edun; ministan tsare-tsaren tattalin arziki da kasafin kudi, Sanata Atiku Bagudu; da kuma Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Olayemi Cardoso, domin bayyana dalilin kin biyan ’yan kwangilar da suka yi aiki da ma’aikatun gwamnati tun daga watan Oktoban shekarar 2024.

Hakazalika, Majalisar ta gayyaci Akanta-Janar na Tarayya da Audita-Janar domin su bayyana tare da sauran jami’an gwamnati a gaban Majalisar a ranar Talata, 13 ga watan Mayu, domin karin bayani kan dalilan jinkirin da kuma gabatar da tsare-tsaren biyan bashin da ake binsu.

Wannan matakin na Majalisar ya biyo bayan amincewa da wani kudiri na gaggawa da dan majalisa Hon. Ezechi Nnamdi daga mazabar Ndokwa ta Jihar Delta ya gabatar yayin zaman majalisar.

A cikin kudirinsa, dan majalisar ya nuna damuwa kan yadda da dama daga cikin ma’aikatu da hukumomin gwamnati ba su samu ko rabin kason kasafin kudin ayyukan ci gaba na shekarar 2024 ba, duk da cewa akwai kudin da aka ware a kasafin.

Leave a Reply