Majalisar zartaswa ta tarayya ta yi wa mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo fatan samun sauki

0 81

Majalisar zartaswa ta tarayya ta yi wa mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo fatan samun sauki, bayan da aka yi masa tiyata sakamakon karaya da ya samu a kashin cinyarsa na dama.
Majalisar zartaswa ta tarayya ta mika sakon fatan alheri a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya fitar jiya a Abuja.
Boss Mustapha ya ce tawagar kwararrun likitoci ne suka gudanar da aikin tiyatar, wacce mai yuwuwa tana da alaka da wani tsohon rauni da ya dade wanda ya samu yayin wasan kwallon squash.
Ya kara da cewa an samu gudanar da aikin cikin nasara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: