Labarai

Kungiyar Ma’aikatan Bankuna da Inshora ta ce za ta bi sahun kungiyar kwadago ta kasa NLC a yajin aikin goyon baya ga ASUU

Kungiyar Ma’aikatan Bankuna, Inshora da Kamfanonin Hada-Hadar Kudi ta Kasa, ta ce za ta bi sahun kungiyar kwadago ta kasa NLC a yajin aikin goyon baya ga kungiyar malaman jami’o’i, ASUU.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugabanta na kasa Anthony Abaakpa da babban sakataren kungiyar Mohammed Sheikh.

Kungiyar ta ce a bayyane take cewa yajin aikin malaman jami’o’I da aka fara tun daga ranar 14 ga watan Fabrairu, zai ci gaba da yin illa ga karatun daliban.

Kungiyar ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sa baki tare da kawo karshen yajin aikin da ake fama da shi.

Kungiyar Kwadago ta NLC ta ce za ta gudanar da zanga-zanga a fadin kasarnan a ranakun 26 da 27 ga watan Yuli domin nuna goyon baya ga kungiyoyin kwadago a jami’o’in gwamnati.

Shugaban NLC, Ayuba Wabba ya bayyana haka a wata takardar da aka rabawa manema labarai mai dauke da sa hannun Emmanuel Ugboaja, babban sakataren kungiyar a Abuja.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: