“Makiyana ne suka sa aka yi garkuwa da ni”, inji sakakken kwamishinan Neja

0 184

Kwamishinan Ma’aikatar Yada Labaran Jihar Neja, Muhammad Sani Idris, wanda ’yan bindiga suka sako bayan kwana hudu da garkuwa da shi ya ce Makiyansa ne suka yi hayar Masu Garkuwa dashi daga Jihar Zamfara.

Kwamishina Muhammad ya yi zargin ’yan bindigar ba su san shi ba ballantana inda yake zaune, amma makiyansa suka dauko hayarsu daga Jihar, suka kwangilar cewa idan ya ba su kudin fansa kasa da Naira miliyan 200 su hallaka shi.

Ya fadi hakan ne jim kadan bayan masu garkuwar sun sako shi a cikin daren ranar Alhamis, yana mai cewa ya yafe musu duniya da lahira.

Kwamishinan ya ce ba su san sunan garin su ba, ba su san sunan karkarar su ba, an bi su ne Zamfara an ba su kudi kuma an ce musu kowanne wata gwamna yana bashi Naira miliyan 200.

A safiyar ranar Litinin masu garkuwa suka yi awon gaba da kwamishinan a gidansa da ke unguwar Babban-Tunga da ke kan Babbar Hanyar Abuja zuwa Kaduna a Jihar Neja.

Ranar Alhamis da dare suka kira iyalansa suka sanar da su inda za su je su dauke shi a cikin dare.

Iyalan nasa da shi kansa ba su ce komai ba game da ko an biya kudin fansa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: