Malam Umar Namadi Ya Ce Gwamnatinsa Za Ta Kasance Bisa Tsarin Adalci Da Tausayawa

0 99

Zababben gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi ya ce gwamnatinsa za ta kasance bisa tsarin adalci da tausayawa.

Namadi ya bayyana hakan ne a sakonsa na karamar Sallah ga al’ummar jihar, cikin wata sanarwa da Daraktan yada labaran mataimakin gwamnan Ahmed Haruna ya fitar.

Ya mika sakon gaisuwar sa ga al’ummar jihar Jigawa tare da addu’ar Allah ya kara musu zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar da ma kasa baki daya.

Ya ce watan Ramadan lokaci ne na tunani da godiya da sabunta imani don haka ya bukaci al’ummar musulmi da su ci gaba da kiyaye kyawawan darussan da suka koya.

Malam Uma ya jaddada kudirinsa na hada kai da daukacin al’ummar jihar, ba tare da la’akari da siyasarsu ba, wajen gina jihar da za ta zama abin alfahari ga al’ummarta. Ya kuma taya al’ummar jihar Jigawa murnar zagayowar wannan rana ta Idin karamar Sallah tare da addu’ar Allah ya karbi ibadun mu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: