Jam’iyyar APC mai mulkin kasar ta mayar da martani game da wata gwamnatin je-ka-na-yi-ka da wasu ‘yan adawar siyasa suka kafa, da nufin kalubalanta da yin gyara ga manufofin gwamnatin kasar.
Matakin da jam’iyyar ta ce bai girgiza ta ko daga mata hankali ba, domin kuwa mataki ne na bigi-bagiro kawai, wato tamkar wani hotoho ne kawai.
Sai dai masana na ganin wannan gwamnatin ta je-ka-na-yi-ka, wadda akan yi irin ta a wasu kasashe, za ta wata sabuwar hanyar zaburar da gwamnatin kasa wajen gudanar da ayyukan da za su amfani al’umma.
Martanin na jam’iyar APC mai mulkin Najeriya, yana zuwa bayan da wani fitaccen masanin tattalin arziki, kuma dan gwagwarmayar siyasa a Najeriya, Farfesa Pat Utomi ya bude wani sabon shafin salon hamayyar siyasa a kasar, ta hanyar kafa gwamnatin je-ka-na-yi-ka.
Inda ya nada ‘ya’yan wasu jam’iyyun hamayya kan mukaman gwamnati irin na dodorido.
Bala Ibrahim, daraktan watsa labarai na kasa na jam’iyyar ta APC, ya ce adawa ce da ba zata yi tasiri ba, iya dai kawai su yi haushi, amma babu wani abu na tada hankali.
“Ai ba su da wannan hurimi, saboda baa gwamnati sai bangarori uku sun hadu.
“Sannna babu wani abin tsoro saboda dama haka ake son dimokuradiyya a samu wadanda za su rika kalubalantar salon mulki domin samun wanzuwa da cigaba a gwagwarmayar biya bukatun al’umma”, in ji Bala Ibrahim.