Al’ummar unguwar Dorayi Ƙarama da kewaye da ke Kano sun miƙa ƙorafi ga Hukumar Tace Fina-Finai ta Jihar Kano kan shirin buɗe wani gidan ɗaukar fina-finai a tsakiyar unguwar.
Ƙorafin ya fito ne ƙarƙashin jagorancin ƙungiyoyi da dama ciki har da Gidauniyar Mata Musulmi ta Kano CCSHD, Arewa Mu Tashi Mu Farka, da Danfodiyo Islamic Center, tare da haɗin gwiwar dattawa, limamai, da masu gidaje.
Da yake jawabi a madadin mazauna unguwar a ranar Talata, Dokta Yusuf Ibrahim, ya bayyana damuwarsu kan yiwuwar tasirin buɗe irin wannan wurin ga tsaro, zaman lafiya da tarbiyyar matasa, musamman duba da ƙalubalen tsaro da yankin ya taɓa fuskanta a baya.
Ya kuma ce dokokin Hukumar Tace Fina-Finai da ƙa’idojin zamantakewar al’umma sun tanadi cewa dole ne a tabbatar da dacewar irin wannan aiki da muhalli, al’ada da muradun mazauna kafin fara shi.
Dokta Yusuf wanda malami ne a Jami’ar Northwest da ke Kano, ya kuma ce ba wai mutanen unguwar na nuna adawa da ci gaba ba ne, amma suna buƙatar hukumomin da abin ya shafa su gudanar da cikakken bincike tare da dakatar da aikin har sai an tabbatar da bin doka da ka’ida.
Ya ce sun aika kwafin ƙorafin zuwa ga Shugaban Ƙaramar Hukumar Gwale, Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano da Hukumar tsaro ta DSS da Hukumar Hisbah, Hukumar Karɓar Ƙorafe-Ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci, Hukumar Shari’a, Majalisar Malamai, Fadar Sarkin Kano, Hakimin yankin, masu unguwanni da shugabannin masallatai domin ɗaukar matakin da ya dace.
Daga cikin waɗanda suka sanya hannu a madadin dubban al’ummar unguwar a takardar ƙorafin sun haɗa da fitattun malamai da shugabanni ciki har da Farfesa Yahaya Imam na Jami’ar Bayero, Malam Ilyasu Sulaiman na Riyadul Quran, Dokta Abdallah Idris na Dan Fodiyo Islamic Medicine da kuma Sheikh Muhammad Bukhari Ibrahim na Anas Bn Malik Academy.
Sauran sun haɗa da Barista Wada Bashir, Imam Ibrahim Muhammad Bunkure, Malam Aliyu Yahaya Dorayi, Malam Abdurrahman Rabiu Bukar Dorayi, Malam Abdurrahman Sa’id Dorayi da Malam Mujahid Ilyasu Sulaiman.
Al’ummar unguwar sun sake tabbatar da aniyarsu ta ci gaba da kare zaman lafiya, bin doka da oda, tare da haɗin kai da gwamnati domin tabbatar da ci gaba mai ɗorewa da kare kyawawan ɗabi’u a cikin al’umma.
Aminiya ta ruwaito cewa wani ɗan fim mai suna Sultan Abdulrazaq Dorayi ne ya gina gidan a matsayin irin sa na farko a Arewacin Najeriya kuma ake shirin buɗe shi a kwanaki masu zuwa.
Sultan dai shi ne shahararren mai fassarar fina-finan Indiya zuwa harshen Hausa, kuma mai shirya fina-finai a Kannywood.
