Nijar Ta Fice Daga Kotun Hukunta Manyan Laifuka Ta Duniya

0 101

Gwamnatin mulkin soja ta Jamhuriyar Nijar ta miƙa buƙatarta ta ficewa daga Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya, ICCC, a hukumance.

Wannan na zuwa ne watanni tara bayan sanar da aniyarta ta barin kotun.

Nijar ta sanar da aniyarta ta ficewa daga kotun a watan Satumban bara tare da ƙasashen Mali da Burkina Faso.

Kotun mai hedikwata a birnin Hague ta ce ta karɓi buƙatar ficewar Nijar daga cikinta a hukumance a ranar 18 ga watan Yuni, 2026, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.

ICC ta ce ficewar ƙasar ba za ta fara aiki nan take ba, domin dokokin kotun sun tanadi cewa sai bayan shekara guda da miƙa sanarwar ficewar za ta tabbata.

Kotun ta kuma jaddada cewa har zuwa lokacin da ficewar za ta fara aiki, Nijar za ta ci gaba da cika dukkan ƙa’idojin da suka wajaba a kanta a matsayinta ta mamba.

Dukkanin ƙasashen uku na yankin Sahel na ƙarƙashin gwamnatocin soji ne da suka karɓi mulki ta hanyar juyin mulki tsakanin shekarun 2020 da 2023.

Gwamnatocin ƙasashen sun zargi kotun da abin da suka kira salon mulkin mallaka, inda suka ce tana nuna son kai ga ƙasashen Afirka.

Babbar ƙawar ƙasashen uku, wato Russia, ita ma ba ta amince da ikon kotun ba.

Leave a Reply