MDD ta Bukaci Gwamnatin Sudan Ta Yi Bincike Kan Karazanar Kisan Babban Jami’inta a Kasar.

0 80

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga gwamnatin Sudan ta yi bincike kan barazanar kisan da aka yi wa babban jami’inta a kasar.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwa kan wani bidiyo a shafukan sada zumunta, inda wani mutum ya nemi fatawa game da halascin kisan jami’in diflomasiyyar na Majalisar Dinkin Duniyar, Volter Perthes.

Mutumin dai ya yi ta zagi da aibata shugaban shirin majalisar a Sudan a wani wuri da jam’iyyun addini suka jagoranta.

Ya zargi Perthes da cire bangaren masu kaifin kishin addini daga tattaunawar da Majalisar Dinkin Duniya ta jagoranta na dawo da mulki hannun farar hula. Sai dai masu shirya taron sun nesanta kansu da kalaman mutumin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: