Birtaniya Ta Kudiri Aniyar Inganta Musayar Bayanan Sirri Najeriya

0 68

Ministan Sojin kasar Birtaniya James Heappey, ya ce Birtaniyya ta kuduri aniyar inganta musayar bayanan sirri da Najeriya da sauran kasashe domin magance ta’addanci da fashin teku a yankin tafkin Chadi da yankin Gulf na Guinea.
Ministan ya bayyana haka yayin ganawa da yan jaridu a ofishin jakadancin kasar Birtaniya dake Abuja.
Ya kuma ce Birtaniya zata taimakawa sauran kasashen yankin domin samar da dabarun magance kalubalan tsaro
Heappey yace kasar Birtaniya zata taimakawa kasashen yankin wajen samar da hanyoyin dakile matsalolin tsaro.
Ya kuma yi nuni da cewa, kasashen biyu sun yi hadin gwiwa wajen gudanar da ayyukan sojan ruwa tare da rundunar sojojin ruwa ta Birtaniya da ke bayar da tallafi ga Najeriya tare da hadin gwiwar horaswa da kuma bunkasa aiki tare a yankin Gulf.
Ya kuma kara da cewa dukkan kasashen biyu zasu ci gaba da kara kaimi wajen inganta tsaron yankin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: