Ministan Shari’a Na Afirka Ta Kudu Bazai Yi Murabus Ba Biyo Bayan Tserewar Mai Laifi Daga Gidan Yari

0 65

Ministan shari’a na Afirka ta Kudu Ronald Lamola ya shaidawa ‘yan majalisar a ranar Alhamis cewa ba zai yi murabus ba saboda tserewar da  mai fyade da kisan kai, Thabo Bester, daga gidan yari mai zaman kansa.

An tafi da Bester zuwa Afirka ta Kudu ranar Alhamis a cikin wani jirgi na musamman da aka yi hayarsa, bayan kama shi a Tanzaniya a makon jiya.

An san shi a matsayin wanda ya yi fyaden a Facebook da yin amfani da dandalin sada zumunta wajen yaudarar wadanda abin ya shafa.

Ministan ya ba da hakuri kan fasa gidan yarin kuma ya ce ya dauki alhaki akan haka.

Ya ce ma’aikatar da ke kula da aikin gyaran hali ya zama wajibi ta tabbatar da cewa an tsare fursunonin har zuwa karshen hukuncin da aka yanke musu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: