Kungiyar ‘Yan Tawayen M23 A Gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango Ta Ce Ba Za Ta Ajiye Makamai Ba

0 122

Kungiyar ‘yan tawayen M23 a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango ta ce ba za ta ajiye makamai ba, muddin ba a yi wata tattaunawa ta siyasa da gwamnati kai tsaye a birnin Kinshasa ba.

Mai magana da yawun ‘yan tawayen, Lawrence Kanyuka ne ya fitar da sanarwar a shafin Twitter bayan shugaban kasar Congo Félix Tshisekedi ya ce ba za a yi wata tattaunawa ta siyasa da ‘yan tawayen ba.

Tshisekedi ya ce a karkashin yarjejeniyar da kasashen yankin suka cimma ana sa ran ‘yan tawayen na M23 za su ruguje kafin su koma rayuwar farar hula.

A karkashin yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla, kungiyar na janyewa daga yankunan da ta kama.

A cikin watanni 18 da suka gabata, kusan kashi uku bisa hudu na mutane fadan ya raba da muhallansu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: