Gwamnatin Nigeria Zata Kashe Naira Miliyan 250 Domin Rage Talauci

0 76

Gwamnatin tarayya ta amince da kashe naira biliyan 250 a bana, a shirinta na rage talauci da take gudanarwa a faɗin ƙasar.
Mataimakin shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo ne ya bayyana hakan yayin wani jawabi da ya yi kan rahoton ci gaban da aka samu a shirin rage talaucin na ƙasa da ake a gaban kwamitin da ya jagoranta ranar Laraba.
Ayyukan da aka tsara aiwatarwa a 2023 ƙarƙashin shirin sun haɗa da Gina gidaje dubu ɗari ga masu ƙaramin ƙarfi, aikin da zai samar da ayyukan yi miliyan ɗaya na kai-tsaye.
Da Samar da ayyuka miliyan huɗu da ɗari biyar na kai-tsaye ko ta hanyar shirin gina hanyoyi a yankin karkara da za su haɗa kasuwannin ƙauye 750 a faɗin Najeriya.
Samar da tallafin naira biliyan tara ga manoma masu ƙaramin ƙarfi a daminar bana karkashin shirin samar da aikin yi a bangaren noma.
yan Najeriya fiye da 8,000 aka ɗauka aikin shimfiɗa tituna a yankunan karkara ƙarƙashin shirin samar da hanyoyi a karkara, inda aka gina hanya 40 da suka ratsa kauyuka 120 a faɗin Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: