Bayan karewar daminar bana wadda tazo da ambaliyar ruwa a sassa daban-daban na kasar nan, yanzu haka hankalin gwamnati da manoma da kuma masu son zuba jari a fannin noma ya karkata ne kacokan kan tunanin shiga noman rani.

Wannan a hasashen masana zai taimaka wajen dakile tsadar kayan abinci da kuma yiwuwar faruwar fari (yunwa).

Ga wasu shawarwari da zasu taimakwa masu son shiga noman rani.

Da farko dai, shi noman rani (Irrigation farming) na tabbatuwane idan akwai abubuwa Kamar haka:
Wadatatcen hanyar ruwa.
Ingantatcen gurin noma (gona)
Ingantatcen iri (seed)
kayan aiki.

Idan ka tanadi wannan abubuwan, to kana bukatar ka fara da guri dan kadan ( mini size) kasan cewar na farin shiga cikin harkar.
Idan kasar gun;


Tabo( clay soil) to zata iya daukar ko wace irin shuka Kamar: Tumaturi, albasa, taruhu da sauran su.


Yashi ( Sandy loamy)
To zata iya daukar Tumaturi, alayyaho, da kankana.
Sai ka duba ka gani.


Amma yana da matukar kyau a cewar wani manomi Malam Shehu Kazaure a shawararsa da sabbin shiga su dauki wuridan kadan, domin gwaji.
a tabbata kuma ana neman shawarar malaman gona.

Allah ya a bada sa’a.

Related Posts

  1. Yusuf zubairu sarawa says:

    Wannan haka yake domin farawa da karamin guri zai taimaka wajen saukin fashintar noman da kuma samun saukin aiki,, kai harma da riba mai yawa

Leave a Reply

%d bloggers like this: