Muhuyi Magaji ya yi alkawarin sake bude binciken bidiyon Ganduje na dala

0 225

Sabon shugaban hukumar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, Barista Muhuyi Magajin Rimin-Gado, ya yi alkawarin sake bude binciken da ake yi wa tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje kan wasu faifan bidiyo da suka janyo cece-kuce.

Jaridar Daily Nigerian ce ta fitar da wasu faifan bidiyo na tsohon Gwamna da ake zargin yana karbar kudade daga hannun ‘yan kwangila.

Tsohon Gwamnan dai ya musanta zargin, yana mai cewa faifan bidiyon an yi shine don a bata masa suna.

Sai dai da yake magana a gidan talabijin na Trust TV’s da Daily Politics, Rimin-Gado, wanda Ganduje ya tsige bayan wasu hatsaniya, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya mayar da shi bakin aiki, wanda ya ce binciken ya zama dole. Ya kuma yi magana kan batutuwa da dama, inda ya musanta cewa an yi amfani da shi wajen tsige tsohon Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi ii daga matsayin sarki.

Leave a Reply