Mukarabban gwamnatina suna da basirar da zasu tafi da Najeriya yadda ya kamata – Tinubu

0 246

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yace mukarabban gwamnatin sa suna da basira da kuma ilimin da zasu tafi da Najeriya yadda ya kamata.

Shugaban kasa ya fadi haka ne jiya,yayinda yake yiwa sabbin Ministocin gwamnatin sa da aka rantsar kwannan jawabi yayin zaman majalisar zartarwa na jiya a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Shugaba Tinubu ya fada sabbin Ministocin cewa yana fatan zasuyi aiki yadda ya kamata domin cikawa yan Najeriya Milyan 200 burin su na samun rayuwa mai kyau da cigaba.

Ya kuma bayyana cewa mukarabban da gwamnatin sa ta zabo, zasu aiki tukuru domin sauke nauyin dake kan su, sannan kuma gwamnatin sa baza ta lamunci uzuri ba ga dukkan wanda yaki yin aikin da aka dora masa.

Shugaban kasa yace, Ministocin an zabo su ne domin suyi aiki na kwarai,da cika manufofin sa na dawo da tattalin arzikin kasar nan, inganta tsaro da zaman lafiya da wadata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: