Za’a samu ambaliyar ruwa a wasu jihohin kasar nan, nan da kwanaki 7 masu zuwa

0 388

Biyo bayan bude dam din Lagdo dake kasar Kamaru, gwamnatin tarayya tace akwai yuyuwa samun ambaliyar ruwa wasu jihohin kasar nan, nan da kwanaki 7 masu zuwa.

Ministar bada agaji da yaki da talauci Betta Edu, itace ta bada wannan tabbacin hasashen a jiya, yayin da ta karbi bakuncin Ministan ruwa da na muhalli, da wasu masu ruwa da tsaki domin tattauna hanyoyin magance matsalar ambaliyar ruwa a Najeriya.

Ministan ta tabbatarwa yan Najeriya cewa za’a raba kayan amfanin yau da kullum ga mazauna yankunan da aka yi hasashen samun ambaliyar.

Sawaba Radio ta rawaito cewa, hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA tayi gargadin samun ambaliyar ruwan sakamakon cika da kogin Riba Basin yayi.

A cewar gargadin,gwamnatin kasar Kamaru ta shirya bude madatsun ruwan Lagdo wanda ya hade dana kogin Benue nan da yan kwanaki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: