Mutum 3 sun mutu a wani sabon hari da wasu yan bindiga suka kai jihar Benue

0 88

Akalla mutane uku ne suka mutu a wani sabon hari da wasu Yan bindiga suka kai kan mutanen garin Tse-Ikyem da ke gundumar Ukemberagya a karamar hukumar Benue.

Mazauna yankin sun shaida wa wakilinmu cewa harin ya faru da misalin karfe 4 na yammacin ranar Asabar, wanda yayi sanadiyyar jikkata wasu mutane da dama.

Wani shugaban al’ummar yankin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce, a ranar 29 ga Oktoba, 2022, da misalin karfe 4 na yamma ne.

Wasu makiyaya dauke da makamai suka kai hari tare da kashe Solomon Ukoom, Eunice Torkwase, Joe Kpei da Mfeseer Iorbume.

Ya kara da cewa mutane da dama sun jikkata yayin harin da aka kai a daidai wurin da aka kashe mutane biyu a ranar Lahadin da ta gabata.

Kakakin rundunar Yan sandan jihar, SP Catherine Anene, ta tabbatar da faruwar harin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: