Babban Hafsan Sojin kasa Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa nan ba da dadewa ba sojoji za su shawo kan kalubalen tsaro da ke addabar kasar nan.
Lagbaja ya bayyana hakan ne yayin bikin rufe taron manyan hafsan soji na kasa da aka hada na biyu da na uku na bana Ajiya Alhamis a jihar Oyo
Ya kuma bayyana aminci da jajircewar sojojin Najeriya ga kundin tsarin mulkin kasar da kuma inganta muradun kasa da kimar kasa.
Ya gode wa mahalarta taron bisa gaskiya da kishin da suka nuna ta hanyar yin amfanin da shawarwari.