Hukumar NDLEA ta kama wani matashi mai shekara 27, Umar Adamu-Umar, da tabar wiwi mai nauyin kilo 9 wadda darajarta ta kai Naira miliyan 10 a Kano.
An cafke shi ne a ranar 6 ga Agusta a kan hanyar Kano–Zariya, yayin da yake safarar ƙunshi 19 na wiwi daga Legas zuwa Kano.
Mai magana da yawun hukumar, Sadiq Muhammad-Maigatari, ya ce matashin ya amsa laifinsa, kuma hukumar ta jima tana bin diddigin shi tun kwanaki biyu kafin kamun.