ICPC da EFCC sun gano Naira Billion 6 da million ɗari 5 da aka danganta da Protocol na Fadar Gwamnatin Kano
Hukumomin yaki da cin hanci da rashawa na ICPC da EFCC sun gano sama da naira biliyan 6.5 da ake zargin an karkatar daga kudaden gwamnatin Kano zuwa hannun Abdullahi Ibrahim Rogo, Daraktan Hulda ga Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Bisa bayanan da kotu ta samu, an ce kudaden an karkatar da su ta hanyar kamfanoni na bogi da aka yi ikirarin suna samun kwangila, amma babu wani aiki da aka yi. ICPC ta riga ta kwato sama da naira biliyan 1.1 daga cikin kudaden.
Bincike ya nuna asusun kamfanonin Rogo da nasa na karan kai sun samu biliyoyin naira, kuma wasu kudade an mayar da su dala ta hannun masu hada-hadar kudade. Kotun Tarayya a Kano ta riga ta ba da umarnin a kwace wani kaso daga cikin kudaden da aka samu a asusunsa.
Rogo ya amsa laifuka a gaban jami’an bincike, amma daga bisani ya garzaya kotu domin hana cafkarsa da gurfanarwa. Sai dai ICPC da EFCC sun bayyana cewa akwai hujjoji masu karfi da ke nuna an yi wawushe kamar yadda jaridar Daily Nigeria ta ruwaito.