Hukumar NAFDAC ta bayyana cewa an gano madarar Cowbell “Our Milk” 12g sachet ta bogi da ke yawo a kasuwannin Najeriya.
A cewar hukumar, Promasidor Nigeria Ltd., wanda ke da lasisin samar da Cowbell, ya bayyana cewa madarar bogin ba daga gare su ba ce, kuma ana amfani da tsohon kwali da suka daina amfani da shi tun watan Satumba 2023.
NAFDAC ta bayyana cewa madarar ta bogi tana da bambanci da ta gaske wajen launi, zane, rubutu, da yadda aka rufe buhun. Hukumar ta ce madarar na iya haifar da mummunan lahani ga lafiya kamar cututtuka, illa ga sassa na jiki, ko ma mutuwa.
Ta bukaci jama’a da su guji siyan madarar da ba ta da tabbacin sahihanci, tare da kai rahoto ga ofisoshin NAFDAC.