Shugaban kwamitin majalisar kan harkokin kiwon lafiya Dr Tanko Sununu ya ce Najeriya ta yi asarar ma’aikatan jinya sama da 1,700 a cikin wata guda.
Sununu ya yi tsokaci ne a gidan Talabijin na Channels TV kan wani kudiri da aka gabatar wanda ke neman yin gyara ga dokar Likitoci ta 2004 don magance magudanar kwakwalwa a bangaren lafiya.
Kudirin dokar ya tilastawa kwararrun likitocin da Najeriya da ta horar da su, gudanar da aikin na tsawon shekaru biyar kafin su samu cikakken lasisi fita waje.
A cewarsa, COVID-19 ya yi barna sosai kan aikin kiwon lafiya a kasar.
A cikin shekarun da suka gabata adadin wadanda suka mutu a kasar a tsakanin ma’aikatan kiwon lafiya yana da yawa, ta yadda hakan ya haifar da guraben aiki da yawa.
- Comments
- Facebook Comments