Pantami Ya Zo Na Biyu A Zaɓen Fidda Gwanin APC Na Gwamnan Gombe

0 221

Tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya samu ƙuri’u 12,120 a zaɓen fidda gwani na kujerar gwamnan Jihar Gombe ƙarƙashin jam’iyyar APC domin babban zaɓen shekarar 2027.

Wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labaran Gwamnan Gombe, Ismaila Uba Misilli ya fitar, ta bayyana cewa Pantami ya zo na biyu bayan Dr. Jamilu Isiyaku Gwamna wanda aka ayyana a matsayin wanda ya lashe zaɓen da ƙuri’u 247,161.

Sanarwar ta ƙara da cewa Pantami ya fafata ne da sauran ‘yan takara ciki har da tsohon Ministan Sufuri, Sanata Sa’id Ahmed Alkali wanda ya samu ƙuri’u 11,612.

Shugaban kwamitin zaɓen fidda gwani na APC a jihar, Sanata Sani Danladi, ya ce an gudanar da zaɓen cikin lumana tare da bin dokokin jam’iyya da kuma ƙa’idojin zaɓe.

Leave a Reply