Jam’iyyar APC ta sanar da sauya ranar gudanar da zaɓen fidda gwani na kujerar gwamna a jihohin Bauchi da Kwara zuwa yau ranar Juma’a 22 ga watan Mayun 2026.
Rahotanni sun nuna cewa jam’iyyar ta kuma dage zaɓen fidda gwani na kujerun Majalisar Dokokin Jihar Zamfara na mazaɓun Maradun I da Maradun II zuwa ranar Lahadi 24 ga watan Mayun 2026.
A wata sanarwa da APC ta fitar, jam’iyyar ta bayyana cewa Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa ne ya amince da sauyin bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki daban-daban.
Jam’iyyar ta ce matakin na daga cikin ƙoƙarin tabbatar da gudanar da zaɓe cikin gaskiya, tsari, zaman lafiya da adalci a jihohin da abin ya shafa.
Sai dai APC ta tabbatar da cewa sauran zaɓukan fidda gwani a faɗin ƙasar nan za su gudana kamar yadda aka tsara tun farko.