PDP ta lashe dukkan kujeru 21 a zaben kananan hakumomin Jihar Adamawa

0 204

Babbar Jam’iyyar Hamayya ta PDP ta lashe dukkan kujeru 21 a zaben kananan hakumomi da aka kammala a Jihar Adamawa a karshen makon nan.

A cewar sakamakon zaben wanda hakumar zaben jihar ta fitar, jam’iyyar PDP ta kuma lashe kujerun kansiloli daga mazabu 226 a jihar, sai jam’iyyar NNPP data yi nasara da samun kujerar kansila 1 a mazabar Demsa dake karamar hakumar Demsa.

Shugaban hakumar zaben Muhammad Umar yace jam’iyya mai mulki a jihar ta lashe kujerun ne rinjaye.

Ya bayyana sakamakon zaben a yammacin jiya Lahdi a hedikwatar hakumar zaben dake Yola Babban Birnin jihar. Umar yace cikin jam’iyyu 19 da suka yi rejista a zaben 12 kawai suka shiga zaben wanda aka gudanar a karshen makon daya gabata.

Jihar Adamawa dai ita ce ta farko data gudanar da zaben kananan hakumomi bayan kotun koli tayi hakunci kan yancin tasarrufi da kudaden kananan hakumomi, wanda ta baiwa gwamnatin tarayya umarnin ta biya kashi 20 ga kudaden kananan hakumomi 774 kai tsaye zuwa asusun nan su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: