Kwamitin zartarwa na Jam’iyyar (PDP) na kasa ya maye gurbin Sanata Iyioricha Ayu a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa.

A taron gaggawa na ranar Talata, kwamitin ya amince da umurnin Babbar Kotun jihar Benue, wanda ya hana Ayu nuna kansa a matsayin Shugaban ‘ jam’iyyar adawar.

Sa’ad da yake jawabi a taron manema labarai a hedkwatar partin dake Abuja a ranar Talata, Debo Ologunagba, Sakataren yada labarai na jam’iyyar, ya ce bayan bincika umurnin Kotun da kyau kuma sun aminta da Shafuffuka 45 (2) na Shari’ar PDP (da aka gyara a shekara ta 2017), kwamitin ya tsai da shawara cewa mataimakin Shugaban jam’iyyar na Ƙasa (shiyyar Arewa), Amb. Umar Ililya Damagum a matsayin sabon shugaban jam’iyyar na kasa baki daya.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: