Peter Obi Ya Isa Kotun Da Aka Fara Sauraron Kararrakin Zaben Shugaban Kasa

0 85

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP) a zaben da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairun daya gabata, Peter Obi, ya isa harabar kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa da ke Abuja, a yayin da aka fara sauraren karar a yau.

Haka kuma a wurin zaman akwai Gwamna Simon Lalong na Jihar Filato, wanda shi ne Darakta Janar na kwamitin yakin neman zaben Tinubu/Shettima a zaben da ya gabata.

Nasarar zababben shugaban kasa Bola Tinubu dai na fuskantar kalubale daga bangaren ‘yan adawa musamman Obi da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana Tinubu na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 8,794,726 inda ya doke Atiku da ya samu kuri’u 6,984,520 da kuma Obi wanda ya samu kuri’u 6,101,533.

Leave a Reply

%d bloggers like this: